Ana samun ƙaruwar cin bashin kuɗin kiran waya tsakanin jama'ar Najeriya

Ana samun ƙaruwar cin bashin kuɗin kiran waya tsakanin jama'ar Najeriya

July 1, 2026 · 10 min

About this episode

This episode discusses the increasing trend of mobile loan uptake among Nigerians, highlighting significant financial statistics.

Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole" na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda ƴan Najeriya suka rungumi ɗaukar bashin kiran waya, wanda wani rahoto ya ce, a bara kaɗai anci bashin kiran waya da ƙudinsu ya kai Naira Tiriliyan 4 da biliyan 61. Wasu bayanai da cibiyar fintech firms Optasia mai tattara alƙaluman shige da ficen kuɗaɗen layukan sadarwa ta fitar a baya-bayan nan, ya nuna yadda ƴan Najeriya waɗanda ke amfani da wayar hannu, a kullum ke tururuwar ciwo bashin katin kira wanda ke ɗauke da kuɗin ruwa. Rahoton cibiyar ya ce a shekarar 2025 kawai ƴan Najeriya sun ci bashin katin kiran waya da ya kai Dala biliyan 3 da miliyan 18 kwatankwacin Naira tiriliyan 4 da biliyan 61, abinda ke haskawa ƙarara cewa adadin ya ƙaru da kaso 12.3 cikin 100 idan an kwatanta da shekarar 2024, wadda ya kasance Naira tiriliyan 4 da biliyan 38. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

People in this episode

Host: Ahmed Abba

Topics covered

Keywords

Mentioned in this episode

Organizations: Optasia

Places: Najeriya

More episodes of Kasuwanci

Explore listener stats, chart rankings, contacts and more on the Kasuwanci podcast page.