
The episode discusses the agreement between Niger and Benin to collaborate against terrorism and the reopening of their borders.
Nijar da Jamhuriyar Benin sun amince da yin aiki a tare don yaƙi da ta’addanci da ke addabar ƙasashen biyu na Yammacin Afirka, yayin da a hannu ɗaya suka kafa wani kwamitin da zai bayar da shawarwari cikin kwanaki 15 a game da yadda za a sake buɗe iyakokin ƙasashen da ke rufe yau kusan shekaru uku. An dai cimma wannan matsaya ce a ziyarar da shugaban Benin Romuald Wadagni ya kai a birnin Yamai ranar talata, inda ya gana da takwaransa na Nijar Janar Abdourahman Tiani. Dangane da hakan ne muka baku damar tofa albarkacin bakin ku ta cikin shirin Ra'ayoyinku Masu Sauraro. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Explore listener stats, chart rankings, contacts and more on the Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare podcast page.