
Senegal ta lashe gasar AFCON karo na biyu bayan nasarar da ta samu kan Morocco
From Wasanni by RFI Hausa
January 19, 2026 · 10 min
About this episode
Senegal wins the AFCON tournament for the second time after defeating Morocco 1-0 in the final.
A jiya Lahadi ne dai aka buga wasan ƙarshe a gasar lashe kofin nahiyar Afrika ta AFCON karo na 35 da ƙasar Morocco ta karɓi baƙunci, inda Senegal ta samu nasara da ci 1 da nema kan Morocco, bayan da ɗan wasanta Pape Alassene Gueye ya jefa kwallo jim kaɗan bayan ƙarin lokacin. Wasan ƙarshen ya kasance mai cike da cecekuce sakamakon tsaiko minti 20 da aka samu, sanadiyar bugun daga kai sai mai tsaron gida da aka bai wa Morocco, lamarin da ya fusata ƴan wasan Senegal ficewa daga fili, amma daga baya Sadio Mane ya dawo da su aka ci gaba da fafatawa. Ɗan wasan gaba na Senegal Sadio Mane ne ya lashe gwarzon ɗan wasa a wannan gasa, Yassine Bounou na Morocco ya lashe gwarzon mai tsaron raga shima abokin wasansa Brahim Diaz da ya zubar da bugun daga kai sai mai tsaron gida ya lashe kyautar takalmin zinari da kwallaye 5. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh............
Topics covered
- sports
- AFCON
- football
- Senegal
- Morocco
Keywords
- AFCON
- Senegal
- Morocco
- Pape Alassene Gueye
- Sadio Mane
- Yassine Bounou
- Brahim Diaz
Mentioned in this episode
Places: Senegal, Morocco, bayan da ɗan
More episodes of Wasanni
- Shiri na musamman kan shirye-shiryen fara gasar lashe kofin duniya · June 8, 2026 · 10 min
- PSG ta lashe Gasar zakarun ta Turai a karo na biyu · June 1, 2026 · 10 min
- Sharhi kan nasarar lashe gasar Premier League da Arsenal ta yi a bana · May 25, 2026 · 10 min
- Yadda aka lashe mafi akasarin gasannin lik-lik na nahiyar Turai · May 18, 2026 · 10 min
- Yadda aka gudanar da gasar Super 4 ta a Najeriya · May 11, 2026 · 10 min
- Matsalolin da suka dabaibaye ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jigawa Golden Stars · May 4, 2026 · 10 min
Explore listener stats, chart rankings, contacts and more on the Wasanni podcast page.